Home General Sabon shugaban ƙaramar hukumar Gwale, Mojo, ya yi barazanar sauka daga kujerarsa

Sabon shugaban ƙaramar hukumar Gwale, Mojo, ya yi barazanar sauka daga kujerarsa

Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwale, Abubakar Muazu Mojo ya yi barazanar ajiye aikinsa na shugabancin karamar hukumar muddin ba’a sauya masa Daraktan Mulki, DPM, na karamar hukumar ba.
jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa tuni dai Shugaban karamar hukumar ta Gwale ya bada umarnin a rufe ofishin DPM din, Danjuma Zubairu Bebeji.
A wani sakon murya da Mojo ya aikewa manema labarai, ya yi ikirarin cewa idan har Daraktan Mulkin bai bar karamar hukumar ba to shi zai bar masa wajen.
Ya kara dacewa manufofin Daraktan Mulkin sun saɓa da tsarin Kwankwasiyya na yi wa jama’a hidima da taimako.
Rahotanni sun baiyana cewa Mojo da DPM ɗin sun jima su na takun saƙa tun lokacin da ya ke Shugaban riko na karamar hukumar ta Gwale kafin a zabe shi a watan Oktoba.
Daga cikin zarge-zargen da Mojo ke yi wa Bebeji har da yi wa karamar hukumar zagon kasa da hana tafiyar da aiki yadda ya kamata, gami da sakaci a wajen aikinsa da hakan ya janyo wasu mahimman takardu su ka ɓata.
Saboda haka ne shugaban karamar hukumar ya ce idan ba a ɗauke Bebeji ba, to shi da majalisar kansilolin sa za su sauka su bar masa wajen.
Sai dai kuma har yanzu ba a ji ta bakin DPM ɗin ba.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp