Home General Ƴan ta’adda sama da dubu 129 suka mika wuya ga sojojin Najeriya...

Ƴan ta’adda sama da dubu 129 suka mika wuya ga sojojin Najeriya cikin watanni 6

Babban Hafsan Hafsoshin Sojoin Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa ƴan ta’addan Boko Haram 129,417 da iyalansu sun mika wuya ga jami’an tsaro tsakanin ranar 10 ga watan Yuli zuwa 9 ga watan Disamban wannan shekara ta 2024.

Babbabn hafsan rundunar sojin ƙasa na Najeriya ya bayyana haka ne a taron tsaro na Afrika karo na 18 da ke gudana a birnin Doha na ƙasar Qatar.

Taron, mai taken: “Haɓaka tsaro don samar da Zaman Lafiya wanda Mista Patrick Agbambu na ƙungiyar Watch Africa Initiative ya shirya, ya samu halartar masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro daga ƙasashen Najeriya da Guinea Bissau da Gambia da Afirka ta Kudu da Kenya da kuma Qatar.

Janar Musa a jawabinsa ya bayyana cewa alkaluman sun hada da mayaka 30,426, mata 36,774, da yara 62,265.

A cewarsa, wannan nasara ta nuna ci gaban da ake samu wajen samun zaman lafiya a tsakanin al’umma da ke bunkasa zamantakewa da tattalin arziki a Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp