Home General Najeriya za ta nemi bashi don cike giɓin naira tiriliyan 13 a...

Najeriya za ta nemi bashi don cike giɓin naira tiriliyan 13 a kasafin kuɗin baɗi

Ministan kuɗi da tattalin arziƙi na Najeriya Wale Edun ya bayyana cewa gwamnatin ƙasar za ta nemi bashin naira tiriliyan 13 don cike giɓin da ke cikin kasafin kuɗin shekara mai zuwa.

A jawabin da ya gabatar gaban manema labarai bayan halartar taron majalisar tattalin arziƙi da ya gudana a fadar shugaban ƙasa ta Villa da ke Abuja, Mr Edun ya ce bashin ne kaɗai hanyar da Najeriya za ta iya magance matsalar ta giɓin kasafin kuɗi a wannan karon.

Jumular kuɗin gudanar da ayyuka da ke cikin kasafin ya kai naira tiriliyan 34 da biliyan 8 daga cikin ƙunshin kasafin na naira tiriliyan 47 da biliyan 9 wanda ke nuna ƙaruwar kashi 36.8 daga kasafin 2024.

Jumullar giɓin da ke ƙunshe a kasafin na bana na matsayin naira tiriliyan 13 da biliyan guda wato kashi 3.39 na ma’aunin tattalin arziƙi na GDP.

A cewar Mr Edun an gudanar da kasafin kuɗin na baɗi ne bisa ga duba ga irin gagarumin ci gaban da ƙasar ta samu ƙarkashin jagorancin watanni 18 da shugaba Tinubu ya shafe a kan kujerar mulkin ƙasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp