Gwamnatin jihar Katsina dake arewa maso yammacin Nijeriya ta yabawa dakarun tsaron kasar da suka hadar da Sojojin Operation FANSAN YAMMA dakarun bataliya ta 17 na rundunar sojojin kasa, jami’an tsaro na sa kai da Vigilanti bisa nasarar tarwatsa maboyar ‘yan bindiga dake Kadoji, Matso-matso, Bagga, Dogon Marke da Takatsaba dake karamar hukumar Jibia.
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da PRNigeria ta samu wadda kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jihar Dr. Nasir Muazu ya fitar aka kuma raba manema labarai a jihar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Wannan dai na zuwa ne bayan wata gagarumar nasara da dakarun suka samu a wani hari da suka kai wa ‘yan bindigar a ranar 4 ga watan janairu, wanda ya kassarar ayyukan ta’addanci a kananan hukumomin Jibia, Batsari da Batagarawa duka a jihar katsina dake fama da matsalar rashin tsaro.
Harin hadin gwiwa ta sama da kasa ya samar da nasarar hallaka ‘yan bindiaga 80, yayin da masu yawa suka tsere da raunikan harbi a jukkunan, inda kuma jamián tsaron sauka tarwata maboyar da wasu cikin makamansu.
Sanarwa ta ce gwamnatin jihar Katsina ta nuna farin cikinta bisa wannan nasarar da aka samu bisa hadin kan jami’an da yunkurinsu na dawo da zaman lafiya a shiyyar arewa maso yamma dake fama da matsalar rashin tsaro.
PRNigeria Hausa











