Hukumomi a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya sun mayar da martani game da bayanin da asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya yi cewa akwai yara dubu 250 da ke fama da matsananciyar yunwa daga cikin yara miliyan daya da dubu dari biyu da aka yi nazari a kansu a jihar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Gwamnatin jihar ta ce lokacin da ta karbi mulkin jihar ta tarar da harkokin kula da lafiya ba kamar yadda ta yi tsammani ba, amma a cewar kwamishinan yada labaran jihar, Mahmud Muhammad Dantawasa sun dauki matakai dai-dai gwargwado.
“Yanzu haka gwamnati na gyara asibitocin matakin farko da suke a karkara guda 62 wadanda yawancinsu angama gyaransu kuma yanzu haka ana raba maganin tamowa a asibitin.”
Gwamnatin ta kuma yi kira ga iyayen yara da su riƙa zuwa wadannan asibitoci domin karɓar maganin tamowar kyauta.











