Shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano, Ambasada Haruna Zago ya rasu bayan fama da rashin lafiya.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Guda cikin hadiman Dan zago, Mukhtar Altukura Gwammaja ne ya shaidawa PRNigeria, ta cikin wata sanarwa, wadda ta ce za’a yi Jana’idar sa da misalin karfe 1 na rana a fadar sarkin Kano Muhammadu Sunusi II dake gidan rumfa a jihar kano.
Dan Zago dai fitaccen dan siyasa ne a jihar Kano, wanda da shi aka riƙa yakin neman zaben tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
A ranar 5 ga watan Yulin 2023 ne dai gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nada Haruna Zago a matsayin Shugaban hukumar kwashe shara ta Kano.
PRNigeria Hausa












