An gudanar da jana’izar Amb. Alhaji Ahmadu Haruna Dan Zago, tsohon shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano.
An gudanar da jana’izar a Kofar Kudu, dake fadar mai martaba Sarkin Kano Dr. Muhammadu Sanusi II.
Jana’izar ta samu halartar fitattun mutane da suka hadar da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Dan Zago, ya rasu yana da shekaru 74, sannan ya bar Mata 4 da yaya 37 sai kuma jikoki da dama.
Bayan kammala jana’izar Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya jagoranci zuwa gidan marigayin, domin yi musu ta’aziyyar rashin da suka yi.
Sauran wadanda suka je ta’aziyyar sun hadar da tsohon gwamnan Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da mataimakin gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo da shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Ismail Jibrin Falgore sun shiga gidan marigayin inda suka yi addu’oi domin nema masa gafarar Allah.












