Home General Mutane 16 ne suka mutu sakamakon hadarin babbar mota a Kano –...

Mutane 16 ne suka mutu sakamakon hadarin babbar mota a Kano – FRSC

Rahotannin daga Jihar Kano na bayyana cewa wani hatsarin babbar mota da ya auku a birnin yayi sanadiyyar mutuwar mutane16.

Hukumar kiyaye aukuwar hadurra ta jihar ta tabbatar da faruwar lamarin ta cikin wata sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na  hukumar, Abdullahi Labaran ya fitar, ya ce hatsarin ya auku ne ranar Alhamis da daddare a kan babbar gadar Muhammadu Buhari da ke unguwar Hotoro.

Abdullahi Labaran ya ce lamarin ya faru sakamakon gudu da direban motar ke yi, lamarin da ya sa ta ƙwace masa a daidai gadar.

Ya ƙara da cewa hatsarin ya rutsa da mutum 71 da motar ke ɗauke da su yayin da mutum 52 suka samu raunuka, mutum 16 kuma suka mutu.

Tuni aka kai waɗanda suka jikkata asibin Murtala da ke birnin na Kano domin ba su kulawar da ta dace.

Hatsarin manyan motoci a kan titunan ƙasar na ƙara haifar da fargaba, inda a lokuta da dama idan motocin suka faɗi ake rasa rayuka da asarar dukiyoyi.

Ko a farkon makon nan ma wata babbar mota ɗauke da dabbobi da faɗi a jihar Neja, da ke arewa ta tsakiyar ƙasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Shin AtikuObi Zasu Iya Tsige TinubuShettima a 2027? Daga Yushau A. ShuaibYadda Shari'ar Masarautar Kano ke Ci gaba da Wakana a Kotun ta ƙoliTawagar Amurka na Shirin Tafiya Pakistan Domin Tattaunawar Sulhu da IranDole Najeriya ta Samu Tsaro ta Kowane Hali - Babban Hafsan TsaroChelsea da Newcastle na Harin Coulibaly, Liverpool na Neman Siyan Marcos SensiBadaƙalar $1.3m: Kotu ta ba EFCC izinin Kama Tsohuwar Ministar jin ƙan Najeriya Sadiya FarouqRaphinha ya Magantu kan Fitar da ƙungiyarsa da aka yi Daga Champion LigRundunar sojin Najeriya ta Musanta bai wa Tsofaffin Mayaƙan Boko Haram MakamaiGwamnatin Tarayya ta Sauya Zarge-Zargen da ta ke yi wa MalamiAn Binne Birgediya Janar Braimah da Sauran Sojojin da Boko Haram ta KasheYaƙin Iran: Hauhawar farashin Kaya a Najeriya ya ƙaruAdadin Matasa 'Yan kwaya da Muka Kama a Shekara 5 - NDLEAJam'iyyar ADC ta Kori Nafi'u Bala GombeRigakafin ƙyanda ya Ceci Yara Miliyan 20 a Afirka - Hukumar Lafiya ta Duniya2027 Ita ce Dama ta ƙarshe da zan Fito Takara - Atiku
X whatsapp