Home General Amurka ta musanta zargin ɗaukar nauyin ta’addancin Boko Haram a Najeriya

Amurka ta musanta zargin ɗaukar nauyin ta’addancin Boko Haram a Najeriya

Amurka ta musanta zargin da ke bayyanata a matsayin mai ɗaukar nauyin ayyukan ta’addancin ƙungiyar Boko Haram a Najeriya, ƙungiyar da ta shafe tsawon shekaru ta na ƙaddamar da jerin hare-hare tare da kashe dubunnan ɗaruruwan mutane da suka ƙunshi fararen hula da ɗimbin jami’an tsaro baya ga tagayyara miliyoyin jama’a a ƙasar ta yammacin Afrika.

Jakadan Amurkan a Najeriya, Richard M. Mills Jr. da ke kawar da wannan zargi gaban manema labarai jim kaɗan bayan wata ganawar sirri da ya yi tare da gwamnonin jihohin Najeriya 36 ya ce Amurka ba ta hannu a ƙungiyar Boko Haram, hasalima ta na taimakawa Najeriya don ganin ta kawar da matsalar.

Tun farko ɗan Majalisar Amurka na jam’iyyar Republican da ke wakiltar Pennsylvania Scott Perry ne ya yi iƙirarin cewa hukumar raya ƙasashe ta Amurka USAID ce ke ɗaukar nauyin ƙungiyoyin ta’addanci a ƙasashe ciki har da Boko Haram ta Najeriya.

A ƙoƙarinsa na kare manufar shugaba Donald Trump game da rushe hukumar USAID, Scott ya ce kaso mai yawa na kuɗin da ake tattarawa da sunan tallafi suna ƙarewa ne a hannun ƴan ta’adda irin ISIS da Al-Qaeda sai kuma boko haram kana ISIS Khorasan.

A cewar Mills Jr, babu wata hujja da ke nuna Amurka na goyon bayan ta’addanci a Najeriya, hasalima akwai tarin hujjoji da ke tabbatar da yadda ta ke taimakawa ƙasar wajen magance matsalolin tsaron da suka fabaibayeta.

Jakadan na Amurka a Najeriya ya ce idan Washington ta samu ko da ƙaramar hujja ce da ke nuna ana karkatar da kuɗaɗen tallafin USAID ko sauran ƙungiyoyi da hukumomin Amurka zuwa ayyukan ta’addanci, ko shakka babu za su jagoranci bincike da haɗin gwiwar Najeriya don hukunta masu hannu a badaƙalar.

Ƙungiyar ta’addancin ta Boko haram ta shafe tsawon shekaru aƙalla 15 a yankin arewa maso gabashin Najeriya da wasu sassa na Chadi da Nijar da Arewacin Kamaru da kuma Mali.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp