Home Labarai Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha na tsahon watannin 6

Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha na tsahon watannin 6

Majalisar dattawan Najeriyar dai ta ɗauki matakin dakatar da sanatar ne har na tsawon watanni shida bisa shawarwarin da kwamitin Ɗa’a da Ladabtarwa da Sauraron ƙorafin Jama’a na majalisar ya bayar, bayan nazari kan ƙorafin da sanata Natasha ta miƙa wa majalisar ranar Laraba.

Shugaban kwamatin, Sanata Neda Imasuen shi ne ya bayar da shawarwarin bayan karanto jerin laifuka da kwamitin ya ce ya samu Sanata Natasha da aikatawa a majalisar.

Da yake karanta bayanin dakatarwar, shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio wanda a kansa ne Sanata Natasha ke ƙorafin cin zarafi na lalata, ya nemi jin ra’ayin ƴan majalisar kan su amince ko su ƙi amincewa da dakatarwar ta tsawon watanni shida amma kuma za a iya rage yawan lokacin idan har ta rubuto takardar neman afuwa. Ƴan majalisar kuma sun amince da hakan.

Da ma dai tunda farko sai da kwamitin na Ɗa’a da Ladabtarwa da Sauraron ƙorafin Jama’a na majalisar ya yi watsi da ƙorafin sanata Natasha bisa dalilan cewa ƙorafin da Sanata Natasha ta shigar ranar Laraba bai cika ƙa’ida ba saboda ita mai ƙorafin da kanta ta sanya hannu kan ƙorafin maimakon ta bai wa wani ya shigar da shi a madadinta, lamarin da ya ce ya lalata ƙorafin nata tun ba a je ko’ina ba.

Ya kuma ƙara da cewa batutuwan da ke cikin ƙorafin na gaban kotu a yanzu haka, wanda ya sa ba za a iya tattauna su ba kuma majalisar ba ta da hurumin sauraron su.

Kafin dai shugaban majalisar ta dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya sanar da dakatar da Sanata Natasha sai da aka bai wa ƴan majalisar dattawan da dama suka faɗi albarkacin bakinsu inda ba tare da ragin ɗaka ba suka goyi bayan hukuncin.

Sai dai shugaban marasa rinjaye na majalisar ta dattawa, Sanata Patrick Abba Moro na jam’iyyar PDP wanda shi ma ya ƙwanƙwashi Sanata Natasha amma ya nemi majalisar ta yi wa ƴar majalisar sassauci inda ya ce a rage tsawon lokacin dakatarwar daga watanni shida zuwa uku.

Sanata Natasha ta yi wuf ta ce “wannan rashin adalci ba zai ɗore ba”, kafin a kashe abin maganarta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp