Home General WHO zata ta bawa Nijeriya maganin cutar kuturta

WHO zata ta bawa Nijeriya maganin cutar kuturta

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce za ta aika magungunan cutar kuturta zuwa Najeriya, bayan magance jinkirin da aka samu, lamarin da ya sa dubban masu ɗauke da cutar a ƙasar suka shafe shekara guda ba tare da samun magani ba.

Najeriya – wadda ta bayar da rahoton samun dubban sabbin waɗanda suka kamu da cutar – ta kasance ba ta da maganin cutar saboda riƙe magungunan da aka yi bayan ɓullo da sabbin dokokin gwaji.

Kuturta cuta ce da ake iya maganinta da magunguna daban-daban. Kuma kasancewa Najeriya ta shafe tsawon shekara guda ba tare da maganin ba, jikin wasu masu ɗauke da cutar ya tsananta, sakamakon cutar da ke yanke yatsun hannu da ƙafa tare da shafar ƙwaƙwalwa.

Da dama cikin marasa lafiyar an sallame su daga asibiti domin komawa gida, wani abu da ke ƙara hatsarin yaɗa cutar.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ta buƙaci Najeriya ta ɗage sabbin dokokin gwajin magungunan, inda yanzu kuma ake sa ran rukunin farko na magungunan su isa ƙasar ranar Asabar daga Indiya.

Cikin fiye da shekara 40 cutar kuturta ta ragu matuƙa a faɗin duniya. Amma Najeriya na bayar da rahoton samun ƙaruwar masu kamuwa da cutar fiye da 1,000 a shekarar da ta gabata.

Akwai fiye da mutum 10,000 da ke kamuwa da cutar cikin shekara guda a ƙasashen Brazil da Indiya da kuma Indonesia.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp