An samu wata fashewa a ɗaya daga cikin manyan layin bututu man Najeriya, da ke garin Bodo na ƙaramar hukumar Gokana da ke jihar Rivers.
A cikin daren jiya Litinin ne dai aka samu fashewar a bututun TNP, da Najeriya ke amfani da shi wajen tura mai tashar mai ta Bonny da ke jihar ta Rivers.
Har zuwa safiyar Talatar nan, ɓangaren da aka samu fashewar na ci da wuta, lamarin da ya sanya bakin haraƙi turnuke sararin samaniya.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Kawo yanzu dai hukumomin ƙasar basu tantance abinda ya haifar da fashewar ba, duk da dai akwai barazanar da tsageran yankin suka yi a kwanan nan na kai wa cibiyoyin mai hari, sakamakon yadda a baya-bayan nan gwamnatin ƙasar taƙi tura wa jihar kuɗaɗenta na wata-wata, bisa rikicin siyasar jihar da ke faruwa tsakanin ɓangaren zartarwa da na dokoki.
Itama dai kakakin rundunar ƴan sandan jihar Grace Iringe-Koko, ta ce basu kammala tattara baranai ba don sanin haƙiƙanin abinda ya faru.











