Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusif, ya yi sabbin naɗe-naɗe tare da ɗaga likkafar wasu mutane a ƙunshin gwamnatinsa.
Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Laraba, inda ya ce canje-canjen zai ƙara gogar da shugabannin gobe masu tasowa da kuma ƙara inganta kyakkyawan jagorancin gwamnatin jihar.
Sabbin naɗe-naɗe sune kamar haka;
1- Akitek Hauwa Hassan Tudun Wada – shugabar hukumar kula da tsara birane ta jihar kano (KNUPDA)
2- Mustapha Muhammad – Sakataren yaɗa Labaran Gwamnan kuma mataimakin kakakin Gwamnan.
3- Auwal Lawan Aramposu – Mataimakin Shugaban hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano (KAROTA).
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
4- Dakta Tukur Ɗaiyabu Minjibir – Mai bawa Gwamnan shawara kan harkokin Noma da Kiwo (Agriculture).
Haka kuma gwamnan ya amince da ɗaga likkafar wasu ƙusoshin gwamnatin guda biyu waɗanda suka haɗar da;
1- Hajiya Zulaihat Yusuf Aji – Mataimakiyar Shugaban gidan rediyon Kano, wanda a baya ta kasance babbar mai bawa Gwamna Shawara kan yaɗa labarai.
2- Injiniya Abduljabbar Nanono – Mataimakin Shugaban hukumar samar da wutar lantarki ta jihar kano KHEDCO, wanda a baya shine Mashawarcin Gwamnan akan sabbin dabarun makamashi.
A ƙarshe gwamnan ya taya su murnar muƙaman da suka samu, har ma ya buƙaci suyi aiki tuƙuru wajen sauke nauyin da aka ɗora musu domin samun nasarar gwamnatin na ciyar da jihar gaba.











