Home General M23 ta sake ƙwace wani yanki a Congo bayan watsi da kiran...

M23 ta sake ƙwace wani yanki a Congo bayan watsi da kiran tsagaita wuta

Shugaban ‘yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda a gabashin Congo ya yi watsi da tayin da Kinshasa da Kigali suka yi na tsagaita wuta cikin gaggawa, yayin da dakarunsa suka shiga cikin yankunan gabashin Congo tare da sake ƙwace garin Walikale mai muhimmanci.

Bayan karɓe ikon wasu manyan birane guda biyu a gabashin ƙasar ta Congo, birnin na Walikale dake da tazarar kilomita 125 daga babban birnin ƙasar Kinshasa wanda ke ɗaya daga cikin masu tarin arzikin ma’adanai da ya shiga kwamar ƴan tawayen na M23.

Garin mai yawan al’umma 15,000 ya faɗa ƙarƙashin ikon ƴan tawayen ne bayan wani ƙazamin faɗa da ya ɓarke a tsakaninsu da dakarun sojin ƙasar ta Jamhuriyyar Congo.

Faɗan, wanda ya samo asali daga kisan kiyashi da aka yi a kasar Rwanda a shekarar 1994 da kuma gogayya kan mallakar arzikin albarkatun ƙasa, shi ne mafi muni a gabashin Congo tun bayan yakin shekarar 1998 zuwa 2003 wanda ya yi sanadin mutuwar miliyoyin mutane.

A yayin da masana suka bayyana cewa wannan yaƙin da ƙasashen Congo da Rwanda da kuma Burundi suka tsunduma cikinsa a wannan shekara, ya munana bisa yadda yake ƙoƙarin bazuwa yankin baki ɗayansa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp