Mai shari’a Binta Nyako na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio da kuma wasu mutum uku daga tattauana batun shari’arsu da manema labarai.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Mai shai’a Nyako ta yanke hukuncin ne ranar Juma’a bayan ƙorafin da lauyan da ke kare Akpabio ya yi cewa Natasha na bin daga wannan gidan talabijin zuwa wancan, don tattaunawa da manema labarai kan shari’arsu, duk da cewa batun yana gaban kotu.
Kotun ta ce daga yanzu babu ɓangaren da zai tattauna da manema labarai dangane da batun.
Nyako ta kuma haramtawa Akpabio da Natasha da kuma lauyoyinsu daga yaɗa zaman shari’ar kai-tsaye a shafukan sada zumunta.











