Gwamnatin Tarayya ta ce za ta ci gaba da sayar wa matatun mai ɗanyen mai da kuɗin naira.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin kuɗi ta tarayya ta fitar a shafinta na X ranar Laraba.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ma’aikatar ta ce tsarin, wanda majalisar zartaswa ta fara amincewa da shi, wani daɗaɗɗen yunkuri ne da aka ɗauki tsawon lokaci ana tsara shi.
A cewar ma’aikatar, masu ruwa da tsaki sun nuna goyon bayansu da kuma tabbatar da ganin tsarin na sayar da ɗanyen mai ga matatu a naira ya tafi daidai.
Tsarin wanda ya buƙaci cinikayyar ɗanyen mai a kuɗin naira, an yi shi ne da zimmar ƙarfafa tattalin arzikin ƙasar da inganta tace mai a ƙasar da kuma daidaita ƙudin ƙasashen waje ta hanyar rage buƙatar dala a cinikayyar ɗanyen mai.
Ma’aikatar ta ƙara da cewa wannan tsari zai kuma janyo hankalin masu zuba jari a ɓangaren tace ɗanyen mai.











