Kungiyar Zago Akida ta jihar Kano ta kai ziyarar ga mataimakin shugaban majalisar dattijan Nijeriya Sanata Barau I Jibril Maliya.
Kungiyar karkashin jagorancin shugabanta Mukhtar BBA Gwammaja ta Kai ziyarar ne a gidan sanata dake birnin tarayyar Nijeriya Abuja a ranar Laraba bisa abin da ta kira managarta ayyukan da sanata yake yiwa Al’ummar jihar kano da kasa baki dai.
Da yake jawabi sanata Barau ya bayyana Jagoran kungiyar ta Zago Akida Marigayi Amb. Hon Alhaji Ahmadu Haruna Zago matsayin jajirtaccen ɗan siyasa bisa irin gudunmawar da ya bashi a fannin siyasar gidan sa.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Sanata Barau ya bayyana cewa “Nima dan Zago Akida ne, tabbas anyi babban rashi na Amb. Alhaji Ahmadu Haruna Zago, amma Zago Akida ba marainiya nace, don zan zame mata gata wajen yi mata dukkan abin da take bukata.
Daga bisani sanata Barau ya Gwangwaje kungiya tlda kyautar kudi har Naira Miliyan 5 tare da bata kyautar mota gami da daukar alkawarin gami da daukar alkawarin samarwa da kungiyar dukkan abinda take bukata.
Da yake jawabi tun da bari shugaban kungiyar Mukhtar B.A Gwammaja ya godewa sanata Barau bisa karancin da ya nunawa ƙungiyar da kuma Marigayi Ambasada Ahmadu Haruna Zago.
Ya kuma bayyana cewa kungiyar zata cigaba da taimakawa kokarin sanatan ta ko wacce fuska.












