Tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi ya yi kira ga ƴan hamayya su riƙa magana kan abin da ya kira shugabanci maras kyau da ƙasar ke fuskanta, yayin da ya ce ta kama hanyar durƙushewa.
Yayin da yake jawabi a taron kwamitin zartaswa na jam’iyyar a Abuja ranar Laraba, Mista Obi ya koka kan yawan talaucin da halin matsi da ake fama da shi a ƙasar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ya ce abubuwa na ƙara lalacewa a ƙasar, kuma lokaci ya yi da za a haɗa kai wajen yin abin da ya dace, farawa daga jam’iyyarsa ta LP.
“Dole mu yi magana idan abubuwa suka lalace, Najeriya na kan hanyar durƙushewa, alƙaluma a bayyane suke, mutane da yawa na ƙara talaucewa, mutanen da a baya ke cin abinci mai kyau, yanzu sun koma mabarata…”.
“A baya idan na zo nan, mutane kan riƙa tambayata abin da nake son ci ko sha domin su kawo min, amma yanzu babu wanda yake tambayata, wannan na nuna halin talaucin da ƙasar nan ke ciki, don haka ya kamata mu tashi tsaye mu hada kai don yin gyara,” in ji Mista Obi.











