Gwamnonin babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya sun nisanta kansu da yunƙurin haɗaka tsakanin jam’iyyarsu da wasu jam’iyyun siyasa.
Ƙungiyar gwamnonin ƙarƙashin gwamnan Bauchi Bala Mohammed ta ce ba za ta haɗe da wata jam’iyya ba da nufin tunkarar zaɓen 2027.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
“Ba za mu shiga wata haɗaka ba da kowa da nufin tunkarar zaɓen 2027,” kamar yadda ƙungiyar gwamnonin PDP ta bayyana a sanarwar da ta fitar bayan taron da suka gudanar a Ibadan jihar Oyo.
Wannan dai ya ci karo da iƙirarin tsohon ɗantakarar jam’iyyar kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar a kwanakin baya inda ya ce suna yunƙurin ƙulla haɗaka da wasu jam’iyyu.
Sanarwar gwamnonin PDP ya nuna akwai saɓanin ra’ayi tsakanin ɓangarensu da na Atiku Abubakar.











