Home General Ma’aikatan Nimet sun dakatar da tashin jirgi a jihar Kano

Ma’aikatan Nimet sun dakatar da tashin jirgi a jihar Kano

Zanga-zangar Ma’aikatan hukumar Nimet a filin jirgin saman Malam Aminu Kano dake jihar kano a Arewa maso yammacin Nijeriya ya dakatar da sauka da tashin jiragen sama filin.

Ma’aikatan hukumar sun gudanar da zanga zangar ne bisa abin da suka kira da jan kafa wajen fara biyan su mafi karancin albashi kamar yadda gwamantin tarayyar Nijeriya ta amince da shi.

A wata ganawa da da jaridar Global tracker ta yi da shugaban kungiyar gamayyar kungiyoyin ma’aikatan na  shiyyar arewa maso yammacin Nijeriya Timoty Meshelia, yace baya ga rashin biyan su mafi karancin albashin, akwai kuma hakkokin ma’aikatan na alawus alawus da aka gaza biya.

Kungiyar ta bawa hukumar gudanar filin jirgin saman na Malam Aminu Kano wa’adin wata guda da ta dauki matakan da suka dace wajen magance matsalolin tattalin arziki da ma’aikatan ke fuskanta da suka hadar da biyan su alawus-alawus da kuma samar musu da ingantaccen yanayin aiki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp