Home General BINCIKE: Shin da gaske ne sarkin Katsina ya kori shirin AGILE saboda...

BINCIKE: Shin da gaske ne sarkin Katsina ya kori shirin AGILE saboda suna saba dokokin addinin muslinci a Jihar?

IKIRARI: wata kafara yada labarai dake yada labaranta a kafar internet ta rawaito labarin dake cewa Mai martaba sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ‘ya kori shirin tallafawa yara mata na AGILE wanda aka fi sani da Adolescent Girls Initiative for Learning and Empowerment daga jihar katsina saboda sabawa dokar addini da koyarwar  al’adun jihar.’

CIKAKKEN LABARIN: Labarin ya ce Mai martaba sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ‘ya kori shirin tallafawa yara mata na AGILE wanda aka fi sani da Adolescent Girls Initiative for Learning and Empowerment daga jihar katsina.

“an dauki matakin ne saboda damuwar da ake da ita kan shirin na karya dokokin addinin muslinci da yunkurin bata tarbiyyar ‘ya’ya mata.”

“ya yi gudanar da wani biki a fadarsa, sarkin ya yi kalaman rashin gamsuwa da shirin.

“AGILE na shirin haramtawa ‘ya’yanmu mata saka hijabi, gami da koyar da su wasu dabi’u da suka ci karo da al’adunmu da addinin mu,”

“Wannan shirin ya ketare dukkan iyaka, don haka ba za mu yadda da irin wannan halayya ba a matsayinmu na shuwagabannin al’umma. Za mu yi dukkan mai yiwuwa don ganin wannan shiri bai cigaba da gudana ba a cikin al’ummar mu,” a cewar sarkin.

Tabbatar da sahihancin labari: an gudanar da cikakken bincike, da ya hadar da bincikar kafar Internet, kiran waya, gami da bincikar kafafen sada zumunta, kuma mun gano cewa babu wani wuri, lokaci, sahihin labari, ko wani taon biki da sarkin katsina da ya firta wannan Magana ga AGILE, wanda shiri ne na bankin duniya domin habaka karatun yara mata a Nijeriya, a jiharsa.

Yayin da PRNigeria ta tuntubi kodinatan shirin na AGILE na jihar Katsina Mustapha Shehu, ya musanta labarin dake cewa sarkin na Katsina ya ki amincewa da shirin a jihar. Ya bayyana labarin matsayin na “karya.”

“Fadar sarkin ta nesanta kanta da labarin da aka wallafa domin sakawa al’ummar shakku. Don haka ina kira ga Al’umma su yi watsi da irin wannan ikirari, su ke yin kokarin bincika sahihancin labara kafin su yada shi.”

PRNigeria ta tabbatar da sahihancin Kalaman na Shehu daga wasu majiyoyi daga fadar sarkin a lokacin da ta tuntubesu.

Amma kuma, dake masu rike da sarautun gargajiya a cikin al’umma, basu da wata rawar takawa ko doka a cikin gwamnati. Basu da wata dama ta yanke hukunci a gwamnatin jihar kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya da aka yiwa gyaran fuska a shekarar 1999 ya yi tanadi.

KAMMALAWA: bisa bayanan da jaridar PRNigeria ta tattara, mai martaba sarkin Katsina alhaji Abdulmumini Kabir Usman, bai dakatar da shirin AGILE a jihar ba bisa yunkurin karya dokokin Addinin da koyarwar Al’ada.

Don haka, PRNigeria ta yanke hukuncin cewa ikirarin dake cewa sarkin Katsina ya dakatar da shirin AGILE a jihar labari ne na “karya”

By PRNigeria

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp