Mataimakin shugaban majalisar dattijan Nijeriya sanata BarauIi. Jibril Maliya ya nada shugaban kungiyar zago akida na jihar Kano Muktar B.A. Gwammaja matsayin maitaimaka masa na musamman.
Wannan na cikin wata takarda da ta fito daga ofishin sanatan mai dauke da sa hannun Mai taimakawa sanatan ta musamman kan harkokin gudanarwa Ngozi Nkemdirim (Mrs) a madadin shugaban ma’aikatan ofishin mataimakin shugaban majalisar wakilan.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Takardar ta ce “Cikin girmamawa ina mai sanarwa da kai cewa an nada ka matsayin mai taimakawa na musamman ga mataimakin shugaban majalisar Dattijan Sanata Barau I. Jibril. Nadin zai fara aiki ne a ranar 1 ga watan Afirilun 2025, har zuwa watan Mayun 2027.”
Kafin nada shi mukamin ya kasance na hannun dama kuma Kuma mataimaki na musamman ga marigayi Amb A.Ahmad Haruna zago akan harkokin yada labarai da aiyuka na musamman, wanda daga bisani ya zama shugaban kungiyar zago akida ta jihar Kano.
Daga bisani sanarwa ta taya Mukhtar Ali (Muktar B.A.A) murna tare da yi masa fatan Alkhairi a nadin da zai taimaki ayyukan sanatan da Nijeriya baki daya.












