Home General Hukumar tace fina-finai ta haramta bikin ‘ƙauyawa’ a jihar Kano

Hukumar tace fina-finai ta haramta bikin ‘ƙauyawa’ a jihar Kano

Hukumar tace fina-finai a jihar Kano ta sanar da haramta bukukuwan Kauyawa da ake yi a faɗin jihar, a wani mataki na ƙarfafa kyawawan ɗabi’u tsakanin al’umma da kuma bin doka.

Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha ne ya sanar da matakin yayin wani taron manema labarai a yau Asabar, inda ya ce an kuma dakatar da dukkan wuraren gudanar da bukukuwan wato ‘event centers’ har sai abin da hali ya yi.

El-Mustapha ya ce wannan mataki da suka ɗauka wani ɓangare ne da hukumar ke yi na ƙarfafa ɗabi’u masu kyau tsakanin al’umma.

“Wannan mataki da muka ɗauka yana cikin tsarin dokar hukumar mu wanda majalisar jiha ta yi wa garambawul da kuma gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya wa hannu,” in ji El-Mustapha.

Ya ƙara da cewa dokokin sun bai wa hukumar tace finai-finai ta jihar Kano damar kula da kuma sa ido kan ayyukan da DJ (waɗanda ke saka waƙoƙi a bukukuwa) ke yi da kuma dukkan wuraren bukukuwa a faɗin jihar Kano.

“Daga yau duk wanda ya shirya biki da sunan ranar Ƙauyawa ya aikata laifi,” in ji El-Mustapha.

Ya kuma yi kira ga shugabannin al’umma da jami’an tsaro, ciki har da Hisbah da ƴan bijilanti da su haɗa-kai da hukumar domin tabbatar da cewa an bi wannan mataki na haramta bukukuwan ƙauyawa sau da kafa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp