Home General Hadarin mota ya yi sanadiyyar matasa 22 ‘yan asalin Kano

Hadarin mota ya yi sanadiyyar matasa 22 ‘yan asalin Kano

Motar da ke ɗauke da ƴanwasan Kano da masu horar da su a gasar wasanni ta ƙasa wato National Sport Festival ta Najeriya ta yi hatsarin a hanyar komawa gida, inda rahotanni suka ce mutum 22 daga cikinsu sun rasu, sannan wasu sun jikkata.

Lamarin ya faru kimanin kilomita 50 zuwa Kano a yau Asabar bayan  da motar ta taso daga jihar Ogun da ke kudu maso yammacin ƙasar bayan an kammala wasannin a ranar Juma’a.

Shi ma Kwamishinan matasa da wasanni na jihar, Mustapha Rabiu Kwankwaso ya bayyana kaɗuwarsa kan hatsarin, inda ya ce lamari ne da ya taɓa jihar baki ɗaya.

A wata sanarwa da kwamishinan ya fitar, ya ce “wannan lamarin abin tayar da hakali ne matuƙa. Muna jajanta wa ƴanuwa da iyalan waɗanda suka rasu da ma mutanen jihar Kano baki ɗaya,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ɗauki ɗawainiyar kula da sauran waɗanda suka ji raunuka.

WADANNAN SUNE SUKA RASU:
1. Abdurrahman Muhd
2. Abdul’aziz Auwalu
3. Nasiru Adam
4. ⁠Ibrahim Salisu
5. ⁠Bashir Bello (Yar gaya)
6. ⁠Imamumalik Umar
7. ⁠Bilal Salisu (Jegus Photography)
8. ⁠Ashiru Shu’aibu
9. ⁠Abdussamad Rabiu
10. ⁠Abubakar Isma’il Yakubu
11. ⁠Bello Muhd
12. ⁠Usaini Garba
13. ⁠Isah Usman Aliyu
14. ⁠Isah Ibrahim
15. ⁠Abdullahi Saleh Trigger
16. ⁠Nasiru Abdullahi
17. ⁠Aminu Muhammad
18. ⁠Shehu Saidu
19. ⁠Usman Muhammad
20. Sani Yusuf
21. ⁠Muhammad Aminu (Alaja)
22. Hamal Dahiru

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp