Rundunar ƴansandan jihar ta tabbatar da harin da wata ƴar ƙunar bakin wake ta kai a babbar kasuwar kifi da ke Konduga, inda ta ce aƙalla mutum 10 sun mutu, duk da wata majiya ta ce aƙalla mutum 20 ne suka mutu, ciki har da ƴan sa-kai da suke taimakon sojoji wajen yaƙin da ƴan ƙungiyar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
A daren Juma’a na 20 ga Yuni, 2025 ne rahotani suka nuna cewa wata ƴar ƙunar bakin waken ta kai harin a garin na Konduga, wanda ke kusa da Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Da yake magana game da harin, mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya yi Allah wadai da harin, sannan ya yi kira ga jami’an tsaro su ɗauki matakin gaggawa.
An ga wasu hotuna da aka jera gawarwakin waɗanda harin ya rutsa da su a lokacin da ake shirin yi musu jana’iza.











