Home Labarai Rundunar ‘yansanda a Kano ta gano Bama-bamai 9

Rundunar ‘yansanda a Kano ta gano Bama-bamai 9

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta tabbatar da gano wasu bama-bamai 9 da ba su fashe ba.

Mataimakin kakakin rundunar na jihar Kano, DSP Hussaini Abdullahi, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar aka raba manema labarai a jihar, inda ya ce an gano bama-baman ne a gurin da bom ya fashe a kusa da wani kamfanin karafa na Yongxing Steel Company, da ke kan hanyar Ring Road ta unguwar Mariri.

A cewar sanarwar, “Bayan gano bama-bamai 7 da ba su fashe ba a baya, an sake bankado wasu guda biyu, wanda hakan ya kai adadin gaba ɗaya zuwa tara”.

Binciken ‘yan sanda ya gano cewa an haɗa bama-baman ne da shara, wadda aka kawo daga Jihar Yobe ba tare da an sani ba, kuma ɗaya daga cikinsu ya fashe yayin da ake sauke kayan a kamfanin.

don haka rundunar ta buƙaci al’umma da su kwantar da hankalinsu kuma su ci gaba da sanar da hukumomin tsaro da zarar sun ga wani abu da ya daure musu kai wanda basu gamsu da shi ba.

A ƙarshe Kwamishinan ‘yan sandan Jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya mika sakon ta’aziyyar sa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu guda biyar, tare da yi wa waɗanda ke jinya a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano fatan samun sauƙi cikin gaggawa.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp