Home General akwai yuwuwar katsewar wutar lantarki a Nijeriya saboda bashi – Kamfanonin samar...

akwai yuwuwar katsewar wutar lantarki a Nijeriya saboda bashi – Kamfanonin samar da wuta

Kamfanonin samar da wutar lantarki a Najeriya sun ce suna iya dakatar da ayyukansu na samar da wuta saboda tarin bashin da ya haura naira tiriliyan 5 da har yanzu gwamnati ba ta biya su ba, wanda ke barazana ga cigaban aikinsu na samar da lantarki a ƙasar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Shugabar ƙungiyar kamfanonin samar da lantarkin, Dr. Joy Ogaji, ta bayyana cewa kamfanonin sun jima suna nuna kishin kasa ta hanyar ci gaba da samar da wuta duk da rashin biyan su kuɗaɗensu, amma yanzu sun gaji.

Ta ce akwai sabon bashi da ya kai naira tiriliyan 1.2 daga wutar da aka samar a farkon rabin shekarar 2025, wanda ya ƙaru kan bashin da suke bin gwamnati zuwa naira tiriliyan 5.2.

Wannan ya haɗa da naira tiriliyan 2 daga shekarar 2024 da kuma bashin da aka gada tun daga 2015 da ya kai naira tiriliyan 1.9.

A cewarta, “Kuɗin da ake kashewa wajen samar da wuta a kowane wata yana kai wa naira biliyan 250, amma gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan 900 kacal a kasafin kuɗin 2025, kuma har zuwa yau ba a samu cikakken tabbacin samun wannan kuɗi ba.”.

Ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya ce “gwamnati na ƙoƙarin rage wani bangare na bashin, amma ba a bayyana yadda hakan zai faru ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp