Home General ‘Yan sandan Jigawa sun kama Dilolin kwaya a jihar

‘Yan sandan Jigawa sun kama Dilolin kwaya a jihar

Rundunar ƴan sanda Jihar Jigawa ta samu nasarar cafke mutane 13 da ta ke zargi da dillancin miyagun ƙwayoyi a jihar dake arewa maso yammacin Nijeriya.

Wannan dai na cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar SP Shiisu Lawan Adam, ya fitar wadda ta ce dakarun rundunar sun gudanar da wani sumame a sassan jihar  daga ranar 2 zuwa 6 ga watan satumbar 2025, wanda aka shirya shi bayan samun wasu bayanan sirrin da hukumar ta yi kan masu safarar miyagun ƙwayoyi da wasu masu  tayar da hankulan jama’ar jihar.

Sanarwa ta kara da cewa dakarun suna gudanar da sumamen ne a sassana jihar da suka hadar da Dutse, Guri, Birnin Kudu, Bamaina, Babura da Roni, kan maɓoyar masu laifin da wuraren da suke gudanar da safarar miyagun ƙwayoyin, inda aka kama mutane 13 waɗanda suka haɗa da Basiru Garba, Ladan Muhammad, Hassan Ali, Abubakar Sa’adu, Ahmad Muhammad, Aminu Hamisu, Muhammad Abdullahi, Suleiman Abdullahi, Abubakar Auwalu, Faruk Abdullahi, Isah Ismail, Hassan Aliyu, da Usman Muhammad – dukkaninsu daga sassa daban-daban na Jigawa da Nguru, Jihar Yobe.

A yayin samamen, jami’an ƴan sandan sun ƙwato miyagun ƙwayoyi iri-iri ciki har da Exol guda (704), Tramadol (264), Diazepam (3), D5 (2,042), roba mai wari (48), tabar wiwi (4 blocks da 148 wraps), wayar Vivo (da ake zargin ta sata ce), farare da jajayen kafso (602), da wasu kayan maye sanfurin ruwa har lita 6.

Sanarwar ta ce an miƙa waɗanda ake zargi zuwa kotu bayan kammala cikakken bincike.

Kwamishinan ƴan sandan Jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ya gargaɗi duk masu aikata miyagun laifuka da su daina ko kuma su fuskanci hukuncin doka, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da bayanai masu inganci domin taimakawa rundunar wajen dakile aikata laifi.

Sanarwar ta ƙare da tabbatarwa jama’a cewa rundunar ƴan sanda na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a dukkan ƙananan hukumomin jihar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp