Home General Ƙungiyar ƙwadago ta TUC ta yi barazanar shiga yajin aiki a Najeriya

Ƙungiyar ƙwadago ta TUC ta yi barazanar shiga yajin aiki a Najeriya

Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya TUC ta yi watsi da matakin gwamnatin tarayya na ƙara kaso 5% cikin 100% kan farashin kowacce litar mai, tana mai kwatanta hakan a matsayin ganganci da mugunta ga tattalin arzikin ƙasar.

A cewar gwamnatin tarayyar ta ɗauki wannan mataki ne don samun kuɗaɗen shiga da za’a yi amfani da su wajen gina hanyoyi da sauran manyan ayyuka a ƙasar.

Tuni dai ƙungiyar ta baiwa gwamnatin wa’adin kwanaki 14 da ta janye wannan matakin, ko kuma ta ɗauki matakin da take ganin ya dace.

A cewarta cikin matakin da zata ɗauka har da rufe manyan sassan gwamnati musamman basu samar da kuɗaɗen shiga.

Ta cikin wata sanarwa da Festus Osifo da kuma Nuhu Toro shugabannin ƙungiyar suka sanyawa hannu, sun ce a halin da ake ciki ƴan Najeriya na cikin ƙangin biyan haraje-haraje barkatai.

Shugabannin ƙungiyar ƙwadagon, sun ce sabon harajin ba abu ne da zai yiwu ba, don haka ya zama wajibi gwamnati ta dakatar da shi.

A cewarsu ƙungiyar har yanzu ƴan Najeriya basu gama farfaɗowa daga ƙangin da cire tallafin man fetur ya jefa su, baya ga lalacewar darajar Naira.

Tuni dai ƙungiyar ta ce ta fara sanar da sassanta na jihohi don shirin tafiya yajin aiki, idan hakan ta kama.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp