Home Labarai Nan gaba za ku ga Amfanin dokar haraji -Tinubu

Nan gaba za ku ga Amfanin dokar haraji -Tinubu

Shugaba Tinubu na Najeriya ya ce idan ƴan Najeriya suka yi haƙuri za a samu rayuwa mai inganci ta hanyar alkilta arziƙin ƙasa yadda ya kamata abin da zai sa ƙasar ta yi fice a duniya a wannan sabuwar shekara ta 2026.

Tinubu ya shaida hakan ne a saƙon sabuwar shekara da ya fitar ranar Alhamis inda ya ƙara da cewa gwamnatinsa ci gaba da gini a kan abin da ta fara na sauye-sauye masu alkairi ga ƴan Najeriya.

“Duk da irin ƙalubalen da duniya ke fuskanta ta fuskar tattalin arziƙi, mun samu gagarumar nasara a 2025 musamman a fannin tattalin arziƙi”.

Dangane kuma da sabuwar dokar haraji da ta fara aiki, Tinubu ya nemi ƴan Najeriya da su ƙara hakuri domin nan gaba kaɗa za su ga alkairin tsarin.

Ya kuma ce ɗaya daga cikin dailan aiwatar da wannan sabon tsarin harajin shi ne kawo sauyi wajen tatsar ƴan Najeriya harajin da ya wuce ƙima.

“Muna kuma son kawo ƙarshen biyan haraji da yawa inda dukkan matakan gwamnati kan karɓi haraji. Na yaba wa jihohin da suka amince da shiga tsarin harajin na bai ɗaya domin sauwaƙe wa jama’a yawan haraje-haraje a kan al’umma da kayan abinci.”

“Sabuwar shekarar ta fara da aiwatar da sauye-sauyen harajin da aka yi domin dasa harsashin Najeriya mai adalci da kuma ƙarfi a fannin kudaɗen shiga,” in ji Tinubu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp