Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano SEMA, ta sanar da cewa za ta ci gaba da kwashe masu matsalolin lafiyar kwakwalwa daga titunan birnin da kewaye.
Bayanai na cewa akwai ɗumbin masu fama da wannan matsala da ke yawo a titunan birnin Kano, cikin mawuycin hali lamarin da ke ƙara matsalar tsaro.
Hukumar ta SEMA ta ce za ta killace su tare da basu magani, kafin a mayar da su garuruwansu.
Hukumar ta kuma ce gwmnatin Kano ta bijiro da aikin kwashe masu larurar kwakwalwar ne domin a basu kulawar da ta dace a matsayinsu na ‘yanadam tare da saita musu rayuwa don su koma cikin iyalansu.
Babban sakataren hukumar, Abdullahi Isyaku Kubarachi, ya shaida wa manema labarai cewa wannan aiki da suka fara dama yana cikin aikace-aikacensu, inda yace hukumar ta gudanar da aikin ne da dadddare da hadin gwiwar wasu hukumomin tsaro, a wasu kananan hukumomin birnin Kano hudu.
Kubarachi ya ƙara da cewa umarnin da gwamnatin Kano ta basu, shi ne su gudanar da aikin tattara masu matsalar kwakwalwar a ƙananan hukumomin cikin birnin Kano tukuna, sannan yace aikin zai taimaka wajen magance matsalar tsaro.
Sakataren hukumar ta SEMA yace mutanen da basu gamsu da bayanansu ba, saboda sha’anin tsaro su mika su ga jami’an tsaro.
Bayanai na cewa masu matsalar kwakwalwa dai suna fama da matsalolin rayuwa a yankunan Najeriya da dama, inda da dama daga cikinsu, matsalar kwakwalwar ba ta yi tsamari ba, amma saboda rashin kulawa da kuma tsangwama suke ta’azzara halin da suke ciki.











