Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL ya ce yana tattaunawa da wata matatar man fetur a ƙasar China domin inganta matatun man fetur na Najeriya.
Babban jami’in gudanarwa na kamfanin, Bayo Ojulari ne ya bayyana haka a ranar Laraba, inda ya ce suna buƙatar ƙwararru ne domin mayar da matatun gwamnatin ƙasar su koma aiki da kyau bayan shekarun da suka ɗauka ba sa aiki yadda ya kamata.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ojulari ya ce nazarin da suka gudanar bayan ya fara aiki ne suka gano cewa ana asarar kuɗi ne maimakon cin riba wajen gudanar da matatun.
Ya ce sun amince da ɗauko ƙwararru waɗanda suka san aikin ɓangaren, maimakon ɗauko ƴan kwangila.
“Shirye-shirye sun yi nisa. Muna ci gaba da tattaunawa da wasu ƙwararru da muke so su inganta mana ayyukan matatun. Kuma gobe wasu daga ciki za su fara zuwa matatun.”












