Home Labarai Badaƙalar Kuɗi: Kotu ta Yanke wa Saleh Mamman Shekara 75 a Gidan...

Badaƙalar Kuɗi: Kotu ta Yanke wa Saleh Mamman Shekara 75 a Gidan Yari

Saleh Mamman

Badaƙalar Kuɗi: Kotu ta Yanke wa Saleh Mamman Shekara 75 a Gidan Yari

 

Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta yanke wa tsohon ministan lantarki a Najeriya shekara 75 a gidan yari kan almundahanar fiye da naira biliyan 33.

Alƙalin James Omotosho ya yanke hukuncin bayan ya samu Mamman da laifin aikata laifuka 12 da hukumar yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa ta’annati EFCC ta tuhume shi da su masu alaƙa da haɗa baki da almundahana.

EFCC ta tabbatar da hukuncin kotun a saƙon da ta wallafa a shafinta na Fesbuk.

Alƙali Omotosho ya ce ya kamata hukuncin zaman gidan yarin ya soma aiki daga ranar da aka kama mai laifin kasancewar an yanke hukuncin ne ba ya harabar kotun.

Kotun ta kuma umarci hukumomin tsaro da su kamo tsohon ministan a duk inda yake sannan kuma a miƙa wa gwamnati kuɗaɗe da dukiyoyin da aka ƙwato daga hannunsa.

Kotun ta kuma nemi Mamman da ya mayar da naira biliyan 22 na kuɗaɗen aikin samar da cibiyoyin lantarki na Mambila da Zungeru.

An gabatar da Mamman gaban babbar kotun tarayya a Abuja cikin Yulin 2024 bisa tuhume-tuhume 12 da ke da alaƙa da haɗin baki da almundahana. Ya musanta aikata zarge-zargen.

Sai dai a lokacin shari’ar, EFCC ta gabatar da shaidu 17 tare da miƙa wasu bayanai gaban kotun.

Hukuncin da aka yanke a yanzu ya kawo ƙarshen wata babbar shari’ar cin hanci da rashawa da ta fara tun bayan kama tare da tsare Mamman da EFCC ta yi a ranar 10 ga Mayun 2021.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp