Home Taska Dakarun Sojin Najeriya Sun Kashe Ƴan Bindiga 3 Sun Ceto Mutane 9...

Dakarun Sojin Najeriya Sun Kashe Ƴan Bindiga 3 Sun Ceto Mutane 9 da akai Garkuwa da su

Rundunar Soji

Dakarun Sojin Najeriya Sun Kashe Ƴan Bindiga 3 Sun Ceto Mutane 9 da akai Garkuwa da su

 

Jami’an tsaron Najeriya sun kashe wasu mutum uku da ake zargin ‘yan bindiga ne, tare da ceto mutum tara da aka yi garkuwa da su a wani samame da suka kai a jihar Kwara, kamar yadda shafin Channels Television mai zaman kansa ya ruwaito a ranar 30 ga Yuli.

An gudanar da samamen ne tare da haɗin gwiwar jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), dakarun tsaron gandun daji da mafarauta da kuma ‘yan sa-kai a yankunan Obbo-Aiyegunle, Ejiu-Ora da Osi da ke ƙaramar hukumar Ekiti a jihar Kwara, kusa da iyakar jihar Neja.

An yi garkuwa da mutanen ne daga al’ummar Eju, kuma ana cikin tafiya da su ta cikin daji zuwa jihar Neja lokacin da jami’an tsaron suka kai dauki.

Jihar Kwara ta fuskanci ƙaruwa a hare-haren da ake kai wa fararen hula da jami’an tsaro cikin watannin baya-bayan nan.

A ranar 22 ga Yuli, Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da kafa sabon bataliyar sojoji a jihar domin yaƙar masu aikata laifuka, ciki har da ‘yan bindiga da kuma ƙungiyar Mahmuda, wadda gwamnati ta bayyana a matsayin wani reshe na Boko Haram..

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Haba, Abba Bichi — Waɗannan Tallace-Tallacen Ranar Haihuwa Sun Wuce Iyaka! Daga Yushau A. ShuaibNAF ta Kaddamar da Aikin Ceto Bayan Jirgin Saman Soja ya Fado a OndoSojoji Sun Kashe Mayakin B'Haram, Sun Kama Wani a GeidamRijistar Masu Kaɗa Kuri'a a Najeriya ta Kai Miliyan 103 - INECMuna Kafa Sabbin Sansanonin Sojoji Domin Kare Al'ummomin da ke Cikin Hatsari – TinubuJirgin Sojojin Sama (NAF) ya Fado a Ondo Dauke da Mutane 32Sojojin Najeriya Sun Kaddamar da Sabbin Bataliyoyi 3 Don Karfafa Tsaro a ZamfaraCOAS ya Nemi Karin Hadin Kan Sojoji da ECOWAS Kan Barazanar Ketare IyakokiSojoji Sun Kai Hari Sansanin Ƴan Ta'adda, Sun Kashe Mutum Ɗaya, Sun Kama Wanda Ake Zargi a Benue Yunwa da Tsananin Rayuwa Sun Sa Ƴan Tawaye 73 da Iyalansu Sun Mika Wuya — HQ TsaroDakarun Soji  Sun Ceto Sojan da Aka Sace a FilatoAn Tattara Bayanai Kan Hare-Haren Ta'addaci 367, An kashe Ƴan Ta'adda 52 a Watan SatumbaNajeriya @66: Gwamnatin Tarayya ta Karkata Kan Cigaba, Ayyukan Yi, da Inganta RayuwaNajeriya @66: Ministan Tsaro ya yi kira ga  Ƴan Najeriya da su Hada kai Domin Zaman Lafiya da TsaroPDP ta Zargi Gwamnatin Inuwa Yahaya da Shirya Katin Mambobi na Bogi Gabanin Zaben Fidda Gwani a Gombe
X whatsapp