Home Taska Ƙungiyar NARD ta yi Barazanar Shiga Yajin Aiki

Ƙungiyar NARD ta yi Barazanar Shiga Yajin Aiki

Ƙungiyar NARD ta yi Barazanar Shiga Yajin Aiki

 

Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa a Najeriya (NARD) ta yi barazanar shiga yajin aiki na sai baba-ta-gani idan har gwamnatin tarayya ba ta biya buƙatunta ba.

NARD ta ce za ta tsunduma yajin aikin ne a ranar 10 ga watan Agusta saboda gaza biyan buƙatunta da suka shafi bashin albashi da inganta walwalarsu da kuma yanayin aiki ba.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ƙungiyar ta cimma wannan matsaya ne a ƙarshen taron Kwamitin zartarwarta da aka gudanar a Gombe daga ranar 26 zuwa 31 ga watan Yuli.

A yayin taron ne wakilan ƙungiyar suka duba yadda aka aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma da gwamnatin tarayya a baya, tare da nazarin matsalolin da ke addabar fannin lafiya a ƙasar.

Shugaban NARD, Dakta Mohammad Usman Suleiman, ya ce ƙungiyar ta nuna rashin gamsuwa da yadda gwamnatin ke tafiyar hawainiya wajen cika alƙawuran da aka yi, duk da tattaunawa da aka shafe watanni ana yi.

Ya ce ƙungiyar ta tsawaita wa’adin yajin aikin har sau huɗu domin bai wa gwamnati damar warware matsalolin, amma ya ce har yanzu yawancin alƙawuran ba a cika su ba.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Haba, Abba Bichi — Waɗannan Tallace-Tallacen Ranar Haihuwa Sun Wuce Iyaka! Daga Yushau A. ShuaibNAF ta Kaddamar da Aikin Ceto Bayan Jirgin Saman Soja ya Fado a OndoSojoji Sun Kashe Mayakin B'Haram, Sun Kama Wani a GeidamRijistar Masu Kaɗa Kuri'a a Najeriya ta Kai Miliyan 103 - INECMuna Kafa Sabbin Sansanonin Sojoji Domin Kare Al'ummomin da ke Cikin Hatsari – TinubuJirgin Sojojin Sama (NAF) ya Fado a Ondo Dauke da Mutane 32Sojojin Najeriya Sun Kaddamar da Sabbin Bataliyoyi 3 Don Karfafa Tsaro a ZamfaraCOAS ya Nemi Karin Hadin Kan Sojoji da ECOWAS Kan Barazanar Ketare IyakokiSojoji Sun Kai Hari Sansanin Ƴan Ta'adda, Sun Kashe Mutum Ɗaya, Sun Kama Wanda Ake Zargi a Benue Yunwa da Tsananin Rayuwa Sun Sa Ƴan Tawaye 73 da Iyalansu Sun Mika Wuya — HQ TsaroDakarun Soji  Sun Ceto Sojan da Aka Sace a FilatoAn Tattara Bayanai Kan Hare-Haren Ta'addaci 367, An kashe Ƴan Ta'adda 52 a Watan SatumbaNajeriya @66: Gwamnatin Tarayya ta Karkata Kan Cigaba, Ayyukan Yi, da Inganta RayuwaNajeriya @66: Ministan Tsaro ya yi kira ga  Ƴan Najeriya da su Hada kai Domin Zaman Lafiya da TsaroPDP ta Zargi Gwamnatin Inuwa Yahaya da Shirya Katin Mambobi na Bogi Gabanin Zaben Fidda Gwani a Gombe
X whatsapp