Gwamnatin Katsina ta Haramta Ayyukan Kungiyar ‘Yan Sa Kai a Fadin Jahar
Gwamnatin jihar katsina da ke arewa maso gabashin Najeriya ta haramta ayyukan kungiyar ‘Yan Sa-kai a fadin jihar baki daya ba tare da wani bata lokaci ba.
A wata sanarwa da mai ba gwamnan jihar shawara na musamman kan harkokin tsaro, Ibrahim Ahmad ya sanya wa hannu, tare da fitarwa a yau Litinin 14 ga watan Fabrairu 2022, gwamnatin ta ce da wannan sanarwa ta umarci ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro su rushe wannan kungiya ta ‘Yan Sa Kai a duk fadin jihar.
Read Also:
Gwamnatin ta ce ta yi hakan ne bisa la’akari da azarbabin da ‘yan kungiyar ke yi wajen aikata miyagun laifuka, da hakan ke kai su ga kisan gilla a kan mutanen da ba su ji ba ba su kuma gani ba, tare da kwashe musu kaya da sunan aikin tsaro na ‘Yan Sa Kai.
Sanarwar ta ce daga yanzu gwamnatin jihar ta amince ne kawai da kungiyar ‘yan sintiri ta Vigilante Group, wadda ke karkashin kulawa da saidon ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da kuma hukumomin gargajiya.
Gwamnatin ta ce daga yanzu ba a yarda kowa ya zartar da wani hukunci da doka ce kawai ya kamata ta yi ba, bisa kowane dalili, illa duk wanda aka kama bisa zargin aikata wani laifi a mika shi ga ‘yan sanda ko wata hukumar tsaro domin daukar matakin da ya dace, idan har akwai bukatar hakan.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 38 minutes 40 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 20 minutes 5 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com