Home Taska Safarar Miyagun Kwayoyi: NDLEA ta yi Martani ga Jawabin Sifeto Janar na...

Safarar Miyagun Kwayoyi: NDLEA ta yi Martani ga Jawabin Sifeto Janar na ‘Yan Sanda Kan Abba Kyari

Safarar Miyagun Kwayoyi: NDLEA ta yi Martani ga Jawabin Sifeto Janar na ‘Yan Sanda Kan Abba Kyari

 

Kakakin hukumar NDLEA ya yi martani bisa kalaman hukumar yan sanda na zargin boye jami’ansu da sukay aiki tare da Abba Kyari.

Jami’n hukumar ya yi alkawarin cewa ana kammala bincike kan lamarin za’a bayyanawa yan Najeriya.

Hukumar hana amfani da miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA ta yi martani da jawabin Sifeto Janar na yan sanda inda yayi kira ga a hukunta jami’an hukumar da suke taimakawa wajen shigo da hodar Iblis Najeriya.

Zaku tuna cewa a ranar Litinin hukumar NDLEA ta garkame dakataccen DCP na yan sanda, Abba Kyari, kan laifin safarar hodar Iblis mai nauyin kilo 25.

Wannan ya biyo bayan damkeshi da hukumar yan sanda tayi kuma ta mikasa tare da sauran yan sandan dake harkallar tare ga hukumar NDLEA.

Sifeto Janar na yan sanda, IGP Usman Baba Alkali, ya yi kira ga Shugaban hukumar hana fasa kwabrin muggan kwayoyi, Janar Buba Marwa (mrty) ya damke jami’ansa dake taimakawa masu safarar kwaya tare da Abba Kyari.

Daily Trust ta ruwaito kakakin hukumar, Femi Babafemi, da cewa hukumar ba zata yi wani rufa-rufa ba, ko wanene sai an tona masa asiri.

Yayinda aka tambayesa shin me yasa ba’a ambaci sunayen jami’an NDLEA da sukayi safarar tare da Abba Kyari ba, Babafemi yace hukumar ba zata boye kowa ba.

Yace:

“Bayan yin abinda ya dace, wani irin rufa-rufa zamu yi? Duk wanda aka kama da laifi zai fuskanci fushin hukuma.Kuma wannan ne ra’ayin Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa.”

“Muna fatan yan Najeriya su bar hukumar ta kammala aikinta kuma muna tabbatarwa yan Najeriya cewa zamu bayyana musu sakamakon binciken.”

Mu muka kama yan kwaya ba NDLEA ba

Dazu mun kawo muku rahoto IGP inda yace jami’an yan sanda ne suka kamasu ba jami’an NDLEA ba, jami’an NDLEA sun barsu sun wuce saboda an basu cin hanci.

A cewarsa, masu safarar kwayar na turawa jami’an NDLEA hotunansu kafin su isa tashar jirgin sama, saboda haka suna ganinsu suke barinsu su wuce.

Yace:

“Jami’an NDLEA sun barsu sun wuce saboda tun kafin su isa Akwa Ibom an turo musu hotunansu, yayinda suke kokarin fita daga tashar jirgin da kwayoyi ne yan sanda suka kamasu.”

“Saboda haka, Sifeto Janar na yan sanda ya bukaci Shugaban hukumar hana fasa kwabrin kwayoyi ya tabbatar ya damke jami’an hukumarsa dake hada baki da yan kwayan kuma ya gudanar da bincike.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp