An Samu Matar da ta Warke Daga Cutar Kanjamau a Amurka

An Samu Matar da ta Warke Daga Cutar Kanjamau a Amurka

Gamayyar wasu masana kimiyya sun samar da hanyar magance cutar kanjamau a kasar Amurka a yanzu.

Rahoton da kafafen yada labarai na waje suka fitar ya bayyana cewa, an samu matar da ta warke sarai daga kanjamau.

Sai dai, a wasu lokuta a 2009 da 2019 an samu wasu mutanen da suka warke daga cutar, ta wata hanyar daban.

Kasar Amurka – Wata mata da ake kira da ‘Majinyaciyar New York’ domin sakaya sunanta, an ba da rahoton cewa ta zama mace ta farko da ta warke sarai daga cutar kanjamau, TheCable ta tattaro.

An ce an sanar da wannan ci gaban ne a ranar Talata 15 ga watan Fabrairu a wani taro kan cututtuka mai taken: ‘Conference on Retroviruses and Opportunistic Infections’, wanda aka gudanar ta yanar gizo.

A cewar kafar labarai ta NBC, majinyaciyar ta sami magani ne a Cibiyar Kiwon Lafiya ta New York-Presbyterian Weill Cornell a kasar Amurka.

An ce ta kamu da cutar kanjamau a 2013, yayin da aka tabbatar da cewa tana dauke da cutar sankarar bargo a 2017.

Ya lamarin yake?

Hadin maganin, wanda aka ce ya kunshi amfani da jinin da aka dauko daga igiyar cibiya, ya mai da hankali ne ga inganta garkuwar jiki.

Hakazalika, rahoton ya ce, an yi amfani da tsarin jinya na haplo-cord transplant, wanda aka samar don fadada damar samar da maganin ciwon daji ga mutanen da ke da cutar jini.

A cewar jaridar New York Times, duk da cewa masu bincike sun ce suna ci gaba da sanya ido kan yadda ake samun murmurewa daga cutar, amma a cikin watanni 14 da suka gabata ba a gano matar tana dauke da cutar kanjamau ba.

Jinyar ta ya zama mai mahimmanci idan aka yi la’akari da cewa mata sun fi yawa daga cikin mutanen da ke dauke da cutar kanjamau a duniya.

Bisa kididdigar da hadin gwiwar shirin Majalisar Dinkin Duniya kan cutar kanjamau (UNAIDS) ta fitar a 2021, “kashi 53 na dukkan mutanen da ke dauke da cutar kanjamau mata ne da yara mata”.

A baya, kafin wannan sabon ci gaba, an ce wasu maza biyu sun warke sarai daga cutar kanjamau a 2009 da 2019, ta hanyar yi musu dashen bargo.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 14 hours 8 minutes 59 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 15 hours 50 minutes 24 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here