Gwamnan Kwara ya yi Magana Kan Sanya Hijabi Cikin Makarantun Jahar
Gwamnan jahar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya bayyana cewa ko shakka babu yana tare da dalibai mata Musulmai kan lamarin sanya Hijabi cikin makarantun jahar.
Yace wannan ita ce matsayarsa saboda shari’o’in da kotu ta yanke kan lamarin da kuma kasancewar Kwara jaha mai daidaito tsakanin addinai kuma jahar da tafi kama da kudu wajen adadin masu addinai mabananta.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Abdulrazaq yace gwamnatinsa kawai doka da gaskiya take bi da kuma nuna adalci tsakanin kowa, sakataren yada labaransa, Rafiu Ajakaye, ya bayyana, rahoton Daily Trust.
Wannan jawabi na Gwamna ya biyo bayan tuhume-tuhumen da Musulmai da Kirista ke yi cewa Gwamnan ya ki bayyana ra’ayinsa kan lamarin saboda siyasa.
Tuni dai iyalan Habeeb Idris, dalibin da aka kashe yayin zanga-zanga a makarantar Oyun Baptsit kwanakin baya sun yi watsi da diyyar N1m da gwamnatin jahar ta basu.
Hakazalika mutum 11 da suka jikkata sun yi watsi da kudi N250,000 da gwamnatin jahar ta basu.











