Home Taska Gwamnatin Tarayya na Shirin Kwaso Daliban ‘Yan Najeriya Dake Zaune a Kasar...

Gwamnatin Tarayya na Shirin Kwaso Daliban ‘Yan Najeriya Dake Zaune a Kasar Ukraine

Gwamnatin Tarayya na Shirin Kwaso Daliban ‘Yan Najeriya Dake Zaune a Kasar Ukraine

Daliban Najeriya mazauna kasar Ukraniya sun kai kuka ga shugaba Buhari ya kwashesu cikin gaggawa.

Daliban sun aika wasikar kar ka kwana ga Buhari saboda an fara kai musu hare-hare a wuraren zamansu.

Gwamnatin tarayya da majalsar wakilai tuni sun yi alkawarin kwaso daliban.

Kungiyar daiban Najeriya dake karatu a kasar Ukraniya sun yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari yayi gaggawan kwashesu daga kasar.

Wannan ya biyo bayan yakin da ya barke tsakanin kasar Rasha da Ukraniya kuma kimanin mutum 50 sun mutu.

A wasikar mai taken, “BUKATA NA GAGGAWA GA SHUGABAN NAJERIYA MUHAMMADU BUHARI” da kungiyar ta aike ranar Alhamis, daliban sun bayyana yankunan da akwai yan Najeriya da aka kaiwa hari, rahoton DailyTrust.

Shugabar NANS dake Ukraniya, Eunice Eleaka, ta rattafu hannu, kan wasikar.

Wani sashen jawabin yace:

“Muna aike wannan wasika ne bisa rikicin Rasha da Ukraniya wanda yayi muni da safiyar nan 24 ga Febrairu 2022 inda aka fara tashin bama-bamai da harbe-harbe a wuraren da yan Najeriya ke zama.”

“Muna rokonka mai girma Shugaba MUHAMMADU BUHARI ka aiko a kwashe daliban Najeriya dake Ukraniya.”

Gwamnatin tarayya zata kwaso yan Najeriya dake zaune a kasar Ukraniya

Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin da take yi na kwashe yan Najeriya dake zaune a Ukraniya sakamakon yakin da ya barke tsakanin kasar da Rasha a ranar Alhamis.

Gwamnati ta ce tana shirya jirgi na musamman da don kwaso su muddin aka bude tashohin jirgi.

Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, a hirar da yayi a tashar NTA yace an tuntubi ofishin jakadancin Najeriya dake Kiev kan shirya yadda za’a kwaso wadanda ke niyyar dawowa gida.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp