‘Yan Bindiga Sun yi Awon Gaba da Limamin Coci da Mutane 7 a Jahar Neja

‘Yan Bindiga Sun yi Awon Gaba da Limamin Coci da Mutane 7 a Jahar Neja

Yan bindiga sun farmaki cocin Salama Baptist Church da ke kauyen Gidigori a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.

Maharan sun yi awon gaba da limamin cocin da wasu mutane bakwai da ke tsaka da ibadah.

Lamarin wanda ya afku a safiyar yau Lahadi na zuwa ne yan sa’o’i kadan bayan farmakin da mahara suka kai wasu kananan hukumomin jihar inda suka kashe mutum 17.

Niger- Yan ta’adda sun yi garkuwa da akalla mutane takwas a yayin da suke yin ibadah a cocin Salama Baptist Church da ke kauyen Gidigori a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.

Wata majiya daga garin ta ce lamarin ya afku ne da misalin karfe 10:00 na safiyar ranar Lahadi, 27 ga watan Fabrairu, jaridar Daily Trust ta rahoto cewa.

Majiyar ta bayyana cewar limamin cocin na cikin wadanda aka yi garkuwa da su.

Rahoton ya kuma kawo cewa cocin na kusa da yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

Lamarin na zuwa ne yan sa’o’i kadan bayan wasu miyagun ‘yan ta’adda sun farmaki kauyukan kananan hukumomin Mashegu, Lavun da Wushishi dake jihar Niger inda suka kashe akalla mutane 17.

An tattaro cewa ama’a da yawa sun yi ta barin gidajensu sakamakon farmakin wanda ya auku daga karfe 12 na rana zuwa karfe takwas na ranar Asabar.

A karamar hukumar Mashegu, kauyukan da aka kai hari sun hada da Sabon-Rami, Igbede, Chekaku, Ubegi, Maishankafi da Poshi.

 

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 15 hours 9 minutes 48 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 51 minutes 13 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here