Home Taska Jami’an Hukumar ‘Yan Sanda a Jahar Kano Sun Kama ‘Dan Sandan Bogi...

Jami’an Hukumar ‘Yan Sanda a Jahar Kano Sun Kama ‘Dan Sandan Bogi da ke Damfarar Mutane

Jami’an Hukumar ‘Yan Sanda a Jahar Kano Sun Kama ‘Dan Sandan Bogi da ke Damfarar Mutane

 

An damke wani matashi mai amfani da kayan yan sanda wajen damfarar yan kasuwa a jihar Kano.

Yan kasuwan sun bayyana cewa yana zuwa ya saya kaya da Taransfan karya sannan ya jiye lambar wayarsa.

Matashin ya amsa laifin da yayi kuma ya yi nadamar abubuwan da yayi.

Bampai, jihar Kano – Jami’an hukumar yan sanda a jihar Kano sun damke wani dan sandan bogi wanda ake zargi da damfarar yan kasuwa ta hanyar Transfa na karya.

Matashin mai suna Yusuf Abdullahi, ya shiga hannu ne bayan wasu daga cikin yan kasuwan da ya damfara suka kai kararsa ofishin hukumar yan sanda.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Abdullahi Kiyawa, ya bayyana wannan matashi a bidiyo tare da yi masa tambayoyi.

Kiyawa yace:

“Wannan mutum akwai korafe-korafe da muka samu daga wajen mutane uku cewa wani ya je da kayan yan sanda ya gabatar da kansa kuma yayi sayayya hannunsu, ya tura kudi basu ga alert be amma ganin yana sanye da kayan yan sanda suka bashi suka karbi lambar wayansa”

“Tun daga nan idan suka kirashi a waya yaki dauka”

Hira da wadanda ya damfara Kiyawa yayi hira da wadanda suka shigar da shi kara don bayyana yadda yayi sayayya wajensu kuma yayi musu Taransfan karya.

Kowanne cikin yan kasuwan sun bayyana kudin kayan da ya damfaresu da kuma yadda suka yi.

Ya sayi kayan N6000 hannun dan kasuwan farko, N25,000 hannun mai takalma, kuma kayan N55,000 hannun mai gas.

Kiyawa ya yi kira ga mutane su daina saurin yarda da mutum don ya sanya kayan yan sanda.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp