‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Sa Kai 63 a Jahar Kebbi

‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Sa Kai 63 a Jahar Kebbi

 

An gudanar da jana’izar kimanin mutum 60 da suka rasa rayukansu sanadiyyar wani harin kwanton ɓauna da ƴan bindiga suka kai wa ƴan sa kai a yankin Zuru da ke cikin jihar Kebbi a arewa maso yammacin Najeriya.

A yammacin ranar Lahadi ne ƴan bindigar suka auka wa ƴan sa kan a kusa da Zirin Daji.

Lamarin ya faru ne a wasu garuruwa na jihar Kebbi da ke kusa da iyaka da jihar Neja bayan kwanton ɓaunar da ƴan bindiga suka yi wa ƴan sa kai, lokacin da ƴan sa kan suka rarake su domin ƙwato dukiyar jama’ar da ƴan bindigar suka yi awon gaba da ita.

Dagacin garin Takita na daga cikin waɗanda suka shaida lamarin, ya kuma ce wa BBC “gaskiya sun musu kwanton ɓauna sun kashe wajen mutum 63.

“Lokacin da suka shigo da fari sun kwashi mutane da dabbobi ana ta ihun ga ɓarayi, to bayan sun wuce sai ƴan sa kan suka bi bayansu don ceto waɗanda suka kwasa.

“To ashe sun yi wa ƴan sa kan kwanton ɓauna sun ɓuya a saman bishiyoyi, da isar ƴan sa kai wajen sai suka buɗe musu wuta suka kashe su sosai.

Ya ce sun tabbatar da adadin waɗanda suka mutun ne bayan kwaso gawarwakinsu don yin jana’iza.

“Ƴan da kan da aka kashe ɗin sun fito ne daga garuruwa daban-daban ciki har da Takita da sauran wasu garuruwan huɗu.

Sai dai ya ce duk da cewa sun samu labarin su ma ɓarayin dajin an kashe wasu daga cikinsu, to ba su da tabbas akan yawan waɗanda aka kashen.

Lamarin dai ya faru ne ranar Lahadi da misalin karfe 8 zuwa 9 kuma an yi jana’izar tasu da misalin ƙarfe hudu na yamma.

Wani shugaban ƴan sa kai na garin Sanci, daya daga cikin garuruwan da lamarin ya shafa ya ce sai da suka ƙirga gawa 63 daga garuruwan Dabai da Magajiyya da Takita da kuma Rafin Zuru.

Shi ma kwamandan ƴan sa kai na ƙaramar hukumar Zuru ya ce bayan kwaso gawarwakin ne sai suka kai ofishin ƴan sanda inda kowane ɓangare suka je suka kwashi gawarwakin ƴan uwansu.

“Lamarin ya shafi yankin Zuru ne gaba ɗaya, an taɓa kowane ɓangare,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa sun samu tarnaƙi sosai wajen kwaso gawarwakin.

Wani mai magana da yawun rundunar yan sanda Najeriya a jihar Kebbi Nafiu Abubakar ya shaida wa BBC cewa ƴan bindigar suna tsere wa hare-haren sojoji ne da ake kai musu a jihar Neja da ke maƙwabtaka a yayin da suka yi artabu da ƴan sa kan.

Sai dai ya ce har yanzu suna tattara bayanai don gano ainihin yawan mutanen da aka kashe.

Hare-haren ƴan bindiga da satar mutane don kudin fansa da satar dabbobi sun zama ruwan dare a arewa maso yammacin Najeriya.

Amma harin baya-bayan nan shi ne mafi muni da ya taɓa faruwa ga ƴan sa kan da ke faɗa da ƴan bindigar a yankin.

 

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 17 hours 58 minutes 20 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 19 hours 39 minutes 45 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here