Bani na Kashe ta ba: Kotu ta yi Watsi da Ikirarin Makashin Hanifa Abubakar
Babbar Kotun Kano ta yi watsi da ikirarin shugaban makarantar su Hanifa Abubakar, Abdulmalik Tanko.
Tanko, wanda da farko ya amsa cewa ya kashe Hanifa, ya bukaci Kotu ta yi watsi da maganarsa domin ya faɗeta ne don tsirar da rayuwarsa.
Sai dai alkalin Kotun, Mai Shari’a Usman Na’abba, ya ce bai gamsu da hujjojin Tanko ba, dan haka ya karbi cewa ba’a tursasa masa ba.
Kano – Babbar Kotun jihar Kano ta fara shirin yanke hukunci game da shari’ar kisan Hanifa Abubakar yar kimanin shekara biyar a duniya, kamar yadda Aminiya ta ruwaito.
Kotun ta yi watsi da ikirarin wanda ake zargi na farko, Abdulmalik Tanko, wanda ya canza maganarsa ta farko, inda ya ce ba shi ne ya kashe Hanifa ba.
Rahoto ya nuna cewa yanzu haka, Kotun ƙarkashin jagorancin mai shari’a Usman Na’abba, na shirin yanke hukunci kan kisan daliba Hanifa.
Read Also:
Alƙalin Kotun na shirin yanke hukunci ne bayan gamsuwa da cewa babu wanda ya tilasta wa wanda ake zargi, shugaban makaranta, Abdulmalik Tanko, ya amince shi ya kashe yarinyar.
Tun da farko Tanko ya roki Kotun ta yi watsi da kalamansa na farko da ya amsa kisan Hanifa, ya kuma kafa hujja da cewa ya yi haka ne domin ceton rayuwarsa daga azabtarwan yan sanda.
Yayin zaman cigaba da sauraron ƙarar, Tanko ya shaida wa Kotu yadda yan sanda suka rinka azabtar da shi kuma suka masa barazanar kisa matukar bai amsa laifin da ake tuhumarsa ba.
Sai dai bayanan Tanko ya saɓa wa na matar da ake zargin su tare, Fatima Jibrin, wacce ta bayyana cewa masu binciken sun ba ta tsoro amma ba su doke ta ba.
A nasu bangare, yan sandan da suka gudanar da bincike sun musanta zargin Tanko, tare da faɗa wa Kotu cewa sun bi hanyoyin da ya dace wajen karban bayanan mutanen da ake zargin.
Kotu ta yi watsi da ikirarin Tanko Mai Shari’a Na’abba, ya yi watsi da ikirarin Tanko, inda yace bai kawo hujjojin da zasu gamsar da Kotu cewa an tursasa masa ba wajen bincike.
Alƙalin ya ce:
“Na gamsu cewa an bi hanyoyin da ya dace wajen karɓan bayanan mutum biyu na farko da ake zargi kuma da yardarsu, saboda haka na karbi bayanan.”
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 46 minutes 34 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 27 minutes 59 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com