Home Taska Bayan Karbar Kudin Fansa N1m: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutumin da Suka...

Bayan Karbar Kudin Fansa N1m: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutumin da Suka Sace a Jahar Kaduna

Bayan Karbar Kudin Fansa N1m: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutumin da Suka Sace a Jahar Kaduna

 

‘Yan bindiga sun halaka wani bawan Allah da suka sace bayan sun karbe kudin fansa.

Labarin mutuwar ya zo ne a daren Talata bayan yan uwan marigayin sun kai ma yan bindigar naira miliyan daya da suka bukata.

Har yanzu akwai sauran mutanen da aka sace su tare a hannun yan bindigar ciki harda wata mai shirin zama amarya.

Kaduna– Yan bindiga sun kashe wani mutum da suka sace bayan sun karbi naira miliyan daya a matsayin kudin fansa daga yan uwansa, Daily Trust ta rahoto.

A watan Fabrairu ne yan bindiga suka farmaki gidan mutumin a yankin Rigachikun da ke karamar hukumar Igabi sannan suka sace shi da wasu a yankin ciki harda mai shirin zama amarya.

A yayin mamayar, an harbe wani jami’in kwastam da ke aiki da FOU Zone B, Kaduna sannan daga bisani ya mutu a asibiti.

Wata mata a yankin ta fada ma Daily Trust cewa labarin mutuwar mutumin ya zo ne a daren Talata bayan yan uwan marigayin sun kai ma yan bindigar kudin fansa.

Ta ce:

“Sun harbe shi bayan sun karbi kudin fansa daga mutumin da ya kai masu kudin. Dukkanin mazauna yankin na cikin alhini bayan sun sami labarin mutuwar.”

An tattaro cewa an yi jana’izar mutumin a garin Unguwar Shanu inda iyalansa ke da zama.

Dailypost ta kuma rahoto cewa har yanzu amaryar da wani mutum daya suna a hannun wadanda suka yi garkuwa da su din.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp