Rikicin Kasashen Biyu: Rasha ta Tabbatar da Kashe Jami’in Sojanta a Ukraine
Hukumomi a Rasha sun tabbatar da mutuwar mataimakin kwamandan a rundunar sojan ƙasar ta Black Sea Fleet, Kyaftin Andrei Paly, a filin yaƙi na garin Mariupol.
Har yanzu ana ci gaba da fafatawa a garin na Mariupol mai tashar jirgin ruwa.
Read Also:
Tun farko sakataren kwaliejin soja ne mai suna Konstantin Tsarenko ya tabbatar da mutuwar sojan a dandalin sada zumunta na Vkontakte (VK).
Gwamnan yankin Sevastopol, Mikhail Razvozhayev, ya faɗa cikin wani saƙon Telegram cewa “Andrei Nikolaevich ya zaɓi ya kare ƙasarmu a matsayin sana’arsa kuma ya rasu saboda mu zauna lafiya nan gaba”.
Rundunar sojan Ukraine ta yi iƙirarin kashe janar-janar na Rasha biyar tun bayan fara ɓarin wuta ranar 24 ga watan Fabarairu. Sai dai janar ɗaya ne kawai Rasha ta tabbaatar da mutuwarsa – Janar Andrei Sukhovetsky.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1485 days 22 hours 45 minutes 51 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1468 days 27 minutes 16 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com