Home WASANNI PSG ta Sha Kashi a Gidan Monaco a Gasar Ligue 1

PSG ta Sha Kashi a Gidan Monaco a Gasar Ligue 1

PSG ta Sha Kashi a Gidan Monaco a Gasar Ligue 1

Paris St Germain ta sha kashi da ci 3-0 a gidan Monaco a gasar Ligue 1 karawar mako na 29 da suka fafata ranar Lahadi.

Wissam Ben Yedder ne ya fara cin kwallo a minti na 25 da fara tamaula, sannan Kevin Volland ya kara na biyu a minti na 68 daga baya Yedder ya kara na uku a bugun fenariti kuma na biyu da ya ci, saura minti shida su tashi daga fafatawar.

Koci, Mouricio Pochettino zai kara fuskantar kalubale a shirin da yake na lashe kofin babbar gasar Faransa ta bana, bayan da Real Madrid ta fitar da PSG daga Champions League a kakar nan.

Pochettino ya maye gurbin Thomas Tuchel ranar 2 ga watan Janairu da nufin zai lashe Champions League, wanda kungiyar ke kishirwar kofin da bata taba dauka ba.

Shi kuwa Tuchel wanda ya koma Chelsea ranar 1 ga watan Janairun 2021 ya lashe Champions League a kakarsa ta farko da jan ragamar kungiyar Stamford Bridge.

Magoya bayan PSG kan yi wa Lionel Messi da Neymar ihu a wasan da suke yi a gida a baya bayan nan, sai dai kuma PSG a kwanan nan akwai damuwa kan rashin kokarin kungiyar a wasannin da take buga wa a waje, wadda ta yi rashin nasara a karawa hudun da ta yi.

Da wannan sakamakon PSG tana nan a matakinta na daya a kan teburin Ligue 1 da maki 65.

Sauran wasannin Paris Germain a kakar bana:

French Ligue 1 Ranar Lahadi 03 ga watan Afirilun 2022

Paris St-G.vLorient

French Ligue 1 Ranar Lahadi 10 ga watan Afirilun 2022

ClermontvParis St-G.

French Ligue 1 Ranar Lahadi 10 ga watan Afirilun 2022

Paris St-GermainvMarseille

French Ligue 1 Ranar Laraba 20 ga watan Afirilun 2022

Angers da Paris St-Germain

French Ligue 1 Ranar Lahadi 24 ga watan Afirilun 2022

Paris St-Germain da Lens

French Ligue 1 Ranar Lahadi 01 ga watan Mayun 2022

Strasbourg da Paris St-Germain

French Ligue 1 Ranar Lahadi 08 ga watan Mayun 2022

Paris St-Germain da Troyes

French Ligue 1 Ranar Asabar 14 ga watan Mayun 2022

Montpellier da Paris St-Germain

French Ligue 1 Ranar Asabar 21 ga watan Mayun 2022

Paris St-Germain da Metz

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp