Home SIYASA Babu Takarar da Zan Fito a 2023 – Babatunde Fashola

Babu Takarar da Zan Fito a 2023 – Babatunde Fashola

Babu Takarar da Zan Fito a 2023 – Babatunde Fashola

Ministan ayyuka da gidaje a Najeriya, Babatunde Fashola, ya ce babu takarar da zai fito a 2023 sai ta shugabancin gidansa.

Ƙungiyoyi da dama sun jima suna kira ga Fashola ya shiga tseren shugaban kasa, amma ya ce matarsa na ‘ya’yans na can suna jiransa.

A cewarsa da zaran wa’adin mulkin su ya ƙare a 2023, zai koma gida a jihar Legas ya huta.

Abuja– Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, yace ya shiga takarar shugaban ƙasa amma na gidansa.

Mai taimakawa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kan harkon Midiya, Tolu Ogunlesi, shi ne ya bayyana kalaman Ministan a wani rubutu a shafinsa na Twitter.

Ministan ya yi wannan furucin ne lokacin da manema labarai suka tambaye shi game da shirin da yake yi yayin da zaɓen 2023 ke gabatowa.

Da yake ba su amsa, Fashola ya ce:

“Ina neman takarar shugaba amma a gida na, Legas zan koma, matata da ‘ya’ya na na can suna jiran shugaban su. Dukkan ma su neman takara ina musu fatan Alkhairi.”

A kwanakin baya, yan Najeriya sun yaɗa jita-jitar cewa tsohon gwamnan jihar Legas ɗin zai shiga tseren takarar shugaban ƙasa a 2023.

Wasu ƙungiyoyin masoya sun fara karaɗe sassan Najeriya da yaƙin neman zaɓen Ministan, inda suka rinka kira gare shi da ya fito takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya.

Amma Ministan ya musanta alaƙa da irin waɗan nan ƙungiyoyi dake goyon bayan cewa ya fito takara.

Fashola ya maida hankali kan sauke nauyin dake kansa

Hadimin ministan, Hakeem Bello, ya bayyana cewa Fashola ya maida hankali ne wajen sauke nauyin dake kan ma’aikatarsa kuma ba za’a raba masa hankali ba.

A jawabinsa ya ce:

“Mai girma Minista ya maida hankalinsa kacokan kan jagorantar tawagarsa na ma’aikatar ayyuka da gidaje domin sauke nauyin da shugaba Buhari ya ɗora musu.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp