Home SIYASA Gwamna Obaseki ya Kori Ma’aikata 513 Daga Bakin Aiki

Gwamna Obaseki ya Kori Ma’aikata 513 Daga Bakin Aiki

Gwamna Obaseki ya Kori Ma’aikata 513 Daga Bakin Aiki

 

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya amince da korar ma’aikata 513 daga bakin aiki waɗan da ke sashin harkokin wasanni.

A wani kundi mai ɗauke da sanarwan korar ma’aikatan, gwamnan ya ce ya ɗauki wannan matakin domin garambawul ga sashin.

Ma’aikatan da korar ta shafa da suka haɗa da yan wasa da masu horarwa da shugabanni, sun fantsama tituna suna zanga-zanga ranar Laraba.

Edo- Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo, ya sallami ma’aikata 513 na sashin wasanni na jihar kuma matakin ya fara aiki tun daga Litinin 21 ga watan Maris, 2022.

Sallamar aikin a cewar rahoton Vanguard, na cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ranar 4 ga watan Maris, 2022, kuma waɗan da lamarin ya shafa ya kunshi manya da ƙananan ma’aikata.

Legit.ng Hausa ta gano gwamnatin na cewa matakin wani bangare ne na kokarin da take na canza salon sashin wasanni zuwa hukumar wasanni ta jihar Edo.

Zamu biya ma’aikatan da aka kora haƙƙinsu – Gwmanati

Sanarwan ta ƙara da cewa gwamnati zata biya ma’ikatan da korar ta shafa hakkokinsu na albashin wata ɗaya.

Hakanan ta ce za’a fara biyan ma’aikatan kuɗin Fanshon su a watan Afrilu, 2020, a rahoton Leadership ma’ikatan da aka sallama sun kai 514.

Ma’aikatan da matakin sallamar ya shafa sun haɗa da, yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle, masu horarwa da kuma na ɓangaren shugabanci.

Wane mataki ma’aikatan suka ɗauka?

A ranar 24 ga watan Maris, 2022, ma’aikatan da gwamnan ya kora suka fito gagarumar zanga-zanga a kewayen filin Samuel Ogbemudia da wasu tituna dake kusa.

Wasu daga cikin mutanen sun ce sun yi mamakin ganin sanarwan cewa an sallame su daga aiki, kuma aka ba su shawaran su sake neman aiki na wucin gadi.

Ɗaya daga cikin yan zanga-zangan, Patience Igbiti, ta ce:

“Sama da shekara 20 ina aiki a matsayin cikakkiyar ma’aikaciya kuma lokaci guda suka kore ni. Na ƙi karban ayyuka da dama a ƙasar waje domin na yi wa jihata aiki. Daga ina ake son na fara yanzu?”

Haka nan kuma wani ma’aikacin da lamarin ya shafa, Friday Aibangbe, ya ce:

“Ina da kwarin guiwar cewa gwamna bai damu da mu ba kwata-kwata. Mun masa aiki muka zaɓe shi kuma muka sadaukar domin shi, amma abin da ya saka mana da shi kenan yanzu.”

Da yake jawabi ga masu zanga-zanga, shugaban hukumar wasanni, Yusuf Ali, ya ɗau alƙawarin kai korafinsu ga gwamnatin jiha.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp