Home Taska An Tsinci Gawar Jarumar Fim a Dakin Otel a Jahar Benue

An Tsinci Gawar Jarumar Fim a Dakin Otel a Jahar Benue

An Tsinci Gawar Jarumar Fim a Dakin Otel a Jahar Benue

Rundunar yan sanda na Jihar Benue ta tabbatar da cewa an tsinci gawar wata Takor Veronica a dakin otel a unguwar Nyinma.

Yan sanda sun ce an tarar da gawarta da tufafi kuma babu alamun rauni a jikinta wadda hakan na nuna akwai yiwuwar ba kashe ta aka yi ba.

Kakakin yan sandan Benue, Cathrene Anene ta ce a halin yanzu an kama mutum uku da ake zargi da hannu a mutuwar amma likitoci za su yi karin haske.

Jihar Benue – An tsinci gawar Jaruma Takor Veronica a cikin wani daki na Otel a Jihar Benue, kamar yadda The Nation ta rahoto.

A cewar rahotanni daban-daban, an gano gawar na Veronica ne kimanin sati baya bayan ta yi bikin zagayowar ranar haihuwarta.

An rahoto cewa an tsinci gawarta ne a wani dakin otel a unguwar Nyinma na Makurdi.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Benue, SP Catherine Anene ta tabbatar da afkuwar lamarin.

An kama mutane uku da ake zargi da hannu a kisar jarumar, Anene

Kakakin yan sandan ta ce an kama mutane uku da ake zargin suna da hannu a mutuwar jarumar.

“An kawo rahoton mutuwar wata mata a otel amma muna jiran bayani daga likitoci. Ba mu ga alamun rauni a jikinta ba. Don haka gwajin likitoci zai sanar da mu sanadin mutuwarta. Matar da ta mutu tana sanye da tufafi; ba mu ga alamar rauni a jikinta ba.

“An kama mutane uku da ake zargi da hannu a wannan, za su bamu karin bayani. Ba za mu iya cewa kashe ta aka yi ba domin ba mu ga alamar rauni ba,” in ji ta.

Abokanta da abokan aiki sun yi ta wallafa sakon ta’aziyya a dandalin sada zumunta.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp